An dauki wannan mataki ne domin taya murnar zagayowar bikin babbar sallah, wanda ya kasance muhimmin bikin gargajiya na al'ummomi masu bin addinin Musulunci na jihar Xinjiang.
Ana sa ran wannan yunkuri zai biya bukatun al'ummomin, musamman ma wadanda ba sa samun kudin shiga mai yawa.
Ana da tashoshin sayar da nama da dama dake wurare daban-daban a birnin Urumqi, kuma an kafa wasu a yankin karkara, domin tallafawa manoma da makiyaya.
Cikin 'yan shekarun nan, hukumomin kasuwanci na jihar Xinjiang sun dukufa wajen kyautata tsarin adana nama a wurare daban-daban na jihar, ta yadda za a samar da nama kan farashi mai rahusa ga mazaunan wurin a lokacin zuwan manyan bukukuwa. (Maryam)