in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar musulunci ta kasar Sin ta shirya liyafar murnar babbar sallah
2015-09-23 21:52:40 cri

Kungiyar musulunci ta kasar Sin a yau Laraba ta shirya liyafa a nan birnin Beijing, don taya musulmi murnar babbar sallah, liyafan da ya samu halartar mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong da ma sauran manyan shugabannin kasar.

A gun lliyafan, shugaban kungiyar musulunci ta kasar Sin Chen Guangyuan ya gabatar jawabi, inda a madadin kungiyar ya mika gaisuwar sallah da fatan alheri ga musulmin kasar Sin da ma kasashen duniya baki daya.

Shugaban tawagar jakadun kasashen Larabawa dake kasar Sin wanda shi ne jakadan kasar Oman Abdullah Saleh Al Saadi da jakadu sama da 40 na kasashen Islama da ke kasar Sin da kuma wakilan masana musulmin ketare a kasar Sin da na musulmin birnin Beijing gaba daya su sama da 300 sun halarci liyafan.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China