in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata sabuwar doka za ta baiwa 'yan jihar Xinjiang damar haihuwar yara 3
2017-07-31 20:13:11 cri

Wani sauyi da aka yi ga dokar kayyade yawan 'ya'ya da al'ummar dake zaune a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake nan kasar Sin, zai baiwa 'yan kananan kabilun yankin, tare da sauran 'yan babbar kabilar Han dake wurin damar haihuwar 'ya'ya har uku.

Mahukuntan jihar dai sun tabbatar da cewa, tanajin dokar da hukumar kayyade haihuwa da tsarin iyali ta kasar ta amincewa, na nuna cewa, ma'aurata dake zaune a birane na iya haihuwar yara biyu, yayin da takwarorinsu na yankunan karkara ke da ikon haihuwar 'ya'ya 3.

A baya dai 'yan kananan kabilu ne kadai ke da damar haihuwar 'ya'ya biyu, yayin da mazauna birane 'yan babbar kabilar Han ke da damar haihuwar da daya tak.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China