in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara girke kayan aikin gina sabon layin dogo zuwa Xinjiang
2017-06-05 10:26:52 cri
A yanzu haka ma'aikata sun fara kai manyan motocin fara aikin hanyar layin dogo wanda ya hada yankin Xinjiang mai cin gashin kai da lardin Qinghai.

Hanyar mai nisan kilomita 1,213, ta hade yankin Golmud a lardin Qinghai da Korla dake Xinjiang, hanyar ita ce ta uku da ta hade Xinjiang da sauran makwabtan larduna. Sauran hanyoyin biyu su ne wadanda suka hade da yankin Urumqi da Lanzhou, babban birnin lardin Gansu, daya hanyar kuma ta hade da yankin Ejina a Mongolia ta cikin gida da Hami dake gabashin yankin Xinjiang.

Hanyar Golmud-Korla mai tazarar kilomita 708 a yankin Xinjiang da kuma kilomita 505 a lardin Qinghai.

Kimanin RMB yuan biliyan 37.64 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 6.15, za'a kashe wajen gudanar da aikin wanda ake sa ran kammala shi cikin shekaru 5. Ana sa ran sashen Qinghai zai fara aiki zuwa karshen shekarar 2018.

Aikin zai taimaka wajen rage adadin nisan dake tsakanin Golmud da Korla daga awa 26 zuwa 12.

Aikin layin dogon zai hade Xinjiang da layin dogo na Qinghai zuwa Tibet.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China