A cewar takardar, mai taken "Hakkin bil-Adam a yankin Xinjiang--ci gaba da kuma nasarorin da aka cimma", tattalin arziki da jin dadin rayuwar al'ummar yankin ya shiga wani sabin babi a tarihi, tun lokacin da kasar Sin ta aiwatar da shirinta na bude kofa da zurfafa gyare-gyare a shekarar 1978.
Takardar ta kuma bayyana cewa, kafin kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, kungiyoyin kabilu a yankin su ne kurar baya a fannin jin dadin rayuwa da batun kare hakkin bin-Adam.
Sai dai a 'yan shekarun nan, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta dauki matakan da suka dace na bunkasa tattalin arziki da rayuwar mazauna yankin. Matakin da ya taimaka wajen bunkasa ci gaba da kuma hadin kan kabilu, da kare muhimman hakkin bil-Adam na dukkan kungiyoyin kabilun dake yankin.
Takadar ta nanata kudurin mahukuntan kasar Sin na ci gaba da raya yankin da al'ummominsa, yayin da kwamitin tsakiya na JKS a nasa bangare ya taka muhimmiyar rawa wajen raya yankin. (Ibrahim Yaya)