in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin mika rijiyoyi 145 da Sin ta gina ga Kamaru
2017-08-20 13:12:45 cri
A ranar 18 ga wata, aka yi bikin mika rijiyoyin da kasar Sin ta gina ga jamhuriyar Kamaru. A yayin bikin, ministan harkokin makamashi da albarkatun ruwa na kasar Kamaru Basile Atangana Kouna, ya bayyana cewa, rijiyoyin da kasar Sin ta gina a kasar Kamaru sun kyautata zaman rayuwar mutanen kasar kwarai da gaske, kuma, ya nuna godiya matuka ga bangaren Sin a madadin gwamnatin kasar Kamaru.

Haka zalika, ya ce, wadannan rijiyoyi 145 da kasar Sin ta gina a kasar Kamaru, sun samar da ruwa mai tsabta ga mazaunan wurin, gwamnati da al'ummomin kasar Kamaru sun gamsu matuka game da shirin tona rijiyoyin, kana sun nuna godiyarsu bisa ga taimakon da gwamnatin kasar Sin ta samar musu.

Bisa labarin da aka samu, an ce, kamfanin gine-gine na Zhongyang, watau reshen kamfanin CGCOC na kasar Sin, shi ne ya dauki alhakin tona rijiyoyin guda 145 a yankin tsakiya da kuma yankin kudancin kasar Kamaru, aikin da ya lashe kudin RMB miliyan 24.5. Haka kuma, an fara aikin ne a watan Maris na shekarar 2016, sa'an nan, aka kammala aikin a makon da ya gabata, bayan kasar Sin da kasar Kamaru sun gudanar da bincike kan rijiyoyin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China