Gwamnan yankin Midjinyawa Bakari ya sanar ta Gidan Rediyon kasar Kamaru cewa, da jiya da misalin karfe 5 agogon wurin, wasu mutane dauke da makamai su biyu wadanda mai iyuwa suke da alaka da kungiyar Boko Haram ne suka kai wannan hari a garin Kolofata dake yankin arewa mai nisa na kasar, wurin dake kusa da kan iyakar Nijeriya da kasar Kamaru.
Harin da dakarun biyu suka kai ya haddasa rasuwar mutane guda 11, ciki har da maharan su biyu, yayin da mutane 30m kuma suka jikkata, kana wasu daga cikinsu suka ji rauni mai tsanani.
A shekarun baya bayan nan, kungiya Boko Haram ta kan kai hare-hare a kasar Nijeriya, har ma da wasu sassan kasashen dake kewayenta, lamarin da ya haddasa mutuwa tare da jikkatar mutane da dama.
Tun daga karshen watan Yuli na shekarar 2016, ya zuwa yanzu, rundunonin sojojin da kasashen Nijeriya, Nijer, Chadi da Kamaru da wasu kasashen da abin ya shafa suka kafa, suna ta arangama da kungiyar Boko Haram a yankunan dake kan iyaka ta kasar Nijer da kasar Nijeriya, domin ganin bayan kungiyar baki daya. (Maryam)