Jirgin dai na dauke ne da dakaru 37, ya kuma yi dakon kayan bukatun yau da kullum, da suka hada da abinci, da makamashi, a kan hanyar sa ta zuwa kan iyakar kasar da Nijar.
Da yake tabbatar da hakan a Litinin din nan, ministan tsaron kasar ya ce sojojin da suka bace, na cikin rundunar ko ta kwana ta BIG. A daya hannun kuma, an cimma nasarar ceto wasu sojojin 3 daga tekun na Atlantika bayan da jirgin su ya nutse a ranar Lahadi. (Saminu)