in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yabawa Sin da ta tallafawa Kamaru wajen warware matsalar 'yan gudun hijira
2017-08-12 13:35:23 cri
Daraktan ofishin Shirin samar da abinci na duniya wato WEP dake kasar Kamaru, Abdoulaye Baldé ya yabawa kasar Sin sakamakon tallafin da ta samar ga 'yan gudun hijirar kasar Afirka ta tsakiya dake Kamaru, inda ya ce kasar Sin na taka muhimmiyar rawa wajen warware matsalar 'yan gudun hijirar shiyyar.

Daraktan ya bayyana haka ne a yayin bikin mika tallafin kayayyaki da aka shirya a Yaounde, babban birnin kasar.

Abdoulaye Balde ya ce yayin da wasu kasashen Afirka, ciki har da Kamaru ke samun taimakon gaggawa daga kasar Sin, a waje guda kuma suna iya koyon fasahohin Sin na samu ci gaba.

A nasa bangaren, jakadan Sin dake Kamaru, Mista Wei Wenhua ya ce, batun 'yan gudun hijira da bakin haure batu ne da ya shafi shiyya-shiyya da kuma duniya baki daya.

Ya ce a matsayin ta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin na mayar da hankali sosai kan batun, kuma ta himmantu wajen warware matsalar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China