in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Rasha
2017-07-05 10:42:49 cri

A jiya Talata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaran aikinsa na kasar Rasha Vladimir Putin a fadar Kremlin dake birnin Moscow na kasar Rasha, inda suka nuna gamsuwa kan bunkasuwar dangantaka da dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu. Sun kuma tsai da kudurin ci gaba da karfafa fahimtar juna da goyon bayan juna, ta yadda za a inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare.

Bugu da kari, a yayin ganawar tasu, shugabannin biyu sun gabatar da wata sanarwa mai taken "bayani kan karfafa hadin gwiwar dake tsakanin jamhuriyar jama'ar kasar Sin da tarayyar kasar Rasha" da kuma wata sanarwa mai taken "bayani game da wasu harkokin kasa da kasa da shiyya-shiyya da kasar Sin da Rasha suka fidda cikin hadin gwiwa".

Daga bisa ni kuma, shugabannin biyu suka gana da 'yan jaridu cikin hadin gwiwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China