in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar da Xi zai kai kasashen Rasha da Jamus za ta bunkasa hadin gwiwar kasashen
2017-06-29 20:21:51 cri
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Huilai ya bayyana cewa, ziyarar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai kai kasashen Rasha da Jamus za ta bunkasa dangantakar dake tsakanin wadannan kasashe.

Mr Li wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, ya ce, a yayin wannan ziyara ana saran shugaba Xi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Puti za su gudanar da tattaunawa kan hanyoyi da manufofin raya dangantakar dake tsakanin kasashensu, da zurfafa hadin gwiwa a fannin siyasa da mutunta juna.

Bugu da kari, ana saran a lokacin da ya ziyarci kasar Jamus, shugaba Xi zai gana da takwaransa na Jamus Frank Walter Steinmeier da shugabar gwamnatin Jamus Angela merkel inda ake saran za su yi musayar ra'ayoyi kan yadda za su zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu, da kuma kungiyar G20 da hanyoyin magance batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Ana kuma saran shugaban Xi zai halarci taron kolin kungiyar G 20, daga bisani kuma ya kalli wasan kwallon kafa tsakanin kungoyin matasan Sin da Jamus.

Shugaba Xi dai zai gudanar da wannan ziyara ce daga ranar 3 zuwa 6 ga watan Yulin, sai kuma taron G 20 na birnin Hamburg daga ranar 7 zuwa 8 ga watan na Yuli.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China