Shugaban na Sin ya isa Berlin ne a jiya Talata, kuma wannan ita ce ziyararsa ta biyu a Jamus.
Haka zalika, shi ne yada zango na biyu da shugaban ya yi a rangadin aiki da yake a nahiyar Turai, inda ya fara tsayawa a Rasha.
Yayin ziyararsa a Jamus, Shugaba Xi zai je birnin Hamburg don halartar taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki wato G20. (Fa'iza Mustapha)