in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya isa birnin Moscow domin fara ziyarar aiki
2017-07-03 20:22:49 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sauka birnin Moscow na kasar Rasha, inda zai fara ziyarar aiki a karo na biyu, tun bayan darewar sa karagar mulkin kasar Sin a shekara ta 2013.

Da yake tsokaci game da hakan yayin wani taron manema labarai, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Huilai, ya ce a wannan karo, shugaban na Sin zai gana da takwaransa na Rasha shugaba Vladimir Putin, kana sassan biyu za su rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannin cinikayya, da tattalin arziki, da zuba jari. Sauran sassan sun kunshi na hadin kai, da watsa labarai da na raya ilimi.

Har ila yau sassan biyu za su sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa, tare da amincewa juna, da tsarin aiwatar da manufofin su na kawance, da hadin kai mai dorewa tsakanin shekarun 2017 zuwa 2020.

Daga Moscow shugaba Xi zai kuma isa Jamus, inda zai halarci taron kungiyar G20 da aka shirya gudanarwa a kasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China