in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya duba rundunar sojin Sin dake Hong Kong
2017-06-30 10:21:27 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kai ziyara barikin rundunar sojin Sin dake yankin Hong Kong, gabanin halartar sa bikin cika shekaru 20 da komawar yankin na Hong Kong bagaren Sin.

Shugaban na kasar Sin ya gane wa idanun sa tsarin aikin dakarun rundunar dake barikin Shek Kong su 3,100, da kuma nau'o'in kayayyakin aikin soji kimanin 100, ciki hadda makamai masu linzami, da jiragen soji masu saukar angulu da aka baje kolin su.

Kimanin 'yan kallo 4,000 daga sassan al'ummar yankin daban daban ne suka halarci ziyarar da shugaban ya kai barikin sojojin. Baya ga wannan, ana tsara cewa shugaban na Sin, zai halarci bikin kaddamar da zababbiyyar gwamnatin yankin ta 5, yayin ziyarar yini 3 da yake gudanarwa a yankin na Hong Kong.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China