in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a samar da karin man fetur da iskar gas tsakanin kasashen duniya
2017-06-27 10:18:38 cri
A jiya Litinin, kwalejin nazarin kimiyya da fasahar zamantakewar al'umma ta kasar Sin ya fidda rahoton ci gaban makamashi na kasashen duniya.

Rahoton ya bayyana cewa, an riga an shiga wani hali na samun isasshen man fetur da iskar gas, kasancewar ana ci gaba da samun karin man fetur da iskar gas a kasashen duniya daban daban, sai dai mai yuwuwa ne bukatun al'ummar duniya ya ragu, don haka a nan gaba, adadin man fetur da iskar gas da za a samar, zai wuce bukatun al'ummomin kasa da kasa, lamarin da zai kawo sauye sauye ga kasuwannin man fetur da iskar gas na kasa da kasa.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu, kasar Amurka tana canja yanayin kasuwannin man fetur da babban karfi, a madadin kungiyar kasashe masu fitar da man fetur zuwa ketare wato OPEC.

A bangaren iskar gas kuma, bisa hasashen da aka yi, ya zuwa shekarar 2030, adadin iskar gas da za a samar daga kasashen duniya zai kai kyubik mita biliyan dubu 5, watau adadin zai karu da kashi 3 bisa dari a ko wace shekara.

Amma, da yake tsokaci kan bukatun al'ummar kasa da kasa, ya ce, ban da kasashen Sin da Indiya da wasu yankunan duniya, karuwar bukatun kasashen Amurka da Turai, ba zai wuce kashi 1 bisa dari ba cikin ko wace shekara, shi ya sa, za a ci gaba da samun iskar gas da ya wuce bukatun duniya cikin dogon lokaci mai zuwa.

Bugu da kari, rahoton ya nuna cewa, sabo da karin bukatun iskar gas da man fetur a yankin Asiya da Pacific, a halin yanzu, yankin Amurka da yankin Turai, da kuma yankin Asiya da Pacific suna kasancewa manyan yankuna guda uku, da suka fi sayen man fetur da iskar gas a duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China