in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya tana shirin kafa runbun bayanai game da makamashi
2017-06-21 09:11:04 cri

Gwamnatin Najeriya tana shirin samar da runbun bayanai wanda zai tattara adadin yankunan kasar da ake da bukatar samar musu da makamashi.

Mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo, shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata a wajen taron musayar ra'ayoyi a Abuja, game da samar da makamashi mai tsabta.

Mukaddashin shugaban kasar ya ce, gwamnati za ta hana jami'an dake samar da hasken lantarki a yankunan karkara na kasar zaman kashe wando, wajen samar da lantarki da mazauna yankunan ke bukata, ta hanyar amfani da makamashi mai tsabta.

Ya shedawa mahalarta taron cewa, za'a samarwa gidaje 20,000 lantarki mai amfani da hasken rana a kashin farko na shirin

Osinbajo ya kara da cewa, wannan shiri zai fadada samar da lantarkin ta hanyar amfani da hasken rana ga magidanta miliyan 1, wanda hakan zai samar da miliyoyin ayyukan yi ga al'ummar kasar.

Kana ya jaddada cewa, wannan shirin zai tattaro dukkan masu ruwa da tsaki wajen yin amfani da hanyoyin samar da makamashi mai tsabta a matsayin hanya ta zahiri wajen habaka ci gaban tattalin arzikin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China