Bankin duniya ya sake duba karuwar hasashensa na farashin man fetur na shekarar 2016
Bankin duniya ya sake duba karuwar hasashensa na tashin farashin danyen man fetur, bisa ganin wata raguwa da wata bukata dake karuwa a tsawon watanni uku na biyu na shekarar 2016. A cikin rahotonta na baya bayan nan na watanni uku kan hangen kasuwar arzikin ma'adinai, hukumar mai bada rance dake da cibiya a birnin Washington ta bayyana cewa farashin gangar danyen mai zai cimma dalar Amurka 43 a shekarar 2016, wata karuwa idan aka kwatanta ga dalar Amurka 41 da aka yi hasashe a watan Afrilu.
Farashin man fetur sun karu da kashi 37 cikin 100 a tsawon watanni uku na biyu na shekarar 2016 dalilin wasu al'amura da dama da suka girgiza samar da man fetur, musamman ma wutar daji a Canada da lalacewar gine ginen man fetur a Najeriya. Muna nan muna jiran ganin farashin man fetur su dan kara karuwa a cikin rabin shekara na biyu na shekarar 2016, idan har harkokin samar da man fetur suka ragu, in ji John Baffes, babban jami'in da ya jagoranci wannan rahoto. (Maman Ada)