A wannan rana, bankin duniya ya fidda sabon rahoto game da makomar hasashen manyan kayayyaki, inda ya ce, a karkashin yanayin kawo sassauci game da kasuwanni, da raguwar darajar dalar Amurka, kasuwar samar da man fetur fiye da kima zai samu sassauci, sabo da haka, an kyautata zaton matsakaicin farashin mai zai kai dalar Amurka 41 kan kowace ganga.
Marubucin rahoton John Baffes ya ce, idan kungiyar OPEC ta kara yawan danyen man da take samarwa, kuma kasashen da ba na kungiyar ba ba su rage hako mai kamar yadda aka yi hasashen ba, farashin man zai iya samun faduwa.(Bako)