in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin hadin gwiwar ayyukan makamashi na Sin da Morocco ya kira taro karo na farko
2017-06-06 12:12:03 cri
A jiya Litinin, kwamitin gudanar da harkokin hadin gwiwar ayyukan makamashi na Sin da Morocco ya yi taro karo na farko a babban birnin kasar Morocco, Rabat.

A yayin taron, bangarorin biyu sun yi tattaunawa kan yadda za a karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin wutar lantarki, makamashi na bola-jari, man fetur da kuma iskar gas da dai sauransu, inda suka kuma cimma sakamako da dama.

A wannan rana, shugaban hukumar makamashi ta kasar Sin Nuer Baikeli da babban jami'i mai kula da harkokin makamashi, ma'adinai da dauwamammen cigaban kasar Morocco Aziz Rabbah sun jagoranci taron cikin hadin gwiwa, kuma, gaba daya akwai wakilan gwamnatoci da kamfanonin kasashen biyu kimanin guda 80 da suka halarci taron.

A yayin taron, bangarorin biyu sun tattauna kan halin da ake ciki yanzu da kuma makomar hadin gwiwar ayyukan makamashi a tsakanin kasar Sin da kasar Morocco, aka kuma cimma ra'ayi daya kan kafa wata tawagar musamman wadda za ta tsara shirin hadin gwiwa kan harkokin makamashi a tsakanin kasashen biyu, da kuma sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a kasar Morocco kan ayyukan makamashi, yayin da bai wa kamfanonin makamashin kasar Morocco goyon baya ta fuskar sha'anin kudi, ta yadda za a inganta hadin gwiwar kasashen biyu kan wannan aiki bisa fannonin daban daban da abin ya shafa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China