Zhang Gaoli ya gabatar da wannan kira ne a Larabar nan, cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin bude taro na 8, na ministoci masu lura da ayyukan bunkasa amfani da makamashi mai tsafta, da taro na 2 na kirkire kirkire a wannan fanni, wanda ya gudana a nan birnin Beijing.
Ya ce Sin na da burin aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki na kasa da kasa, game da aiwatar da ajandar MDD ta samar da ci gaba mai dorewa nan da shekara ta 2030, da ma cimma nasarar yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi.
A wani ci gaban kuma, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada manufar kasar sa, game da bunkasa samarwa da amfani da makashi mai tsafta. Cikin sakon da ya aike yayin taron na yau Laraba, shugaba Xi ya ce bunkasa wannan sashe, zai inganta rayuwar al'ummar duniya yadda ya kamata. (Saminu)