Ministan makamashi, masana'antu da albarkatun ma'adinai na kasar Saudiyya, Khalid Al-Falih ya bayyana a ranar Lahadi a birnin Alger na kasar Aljeriya wani kyakkyaawan fata ga niyyar mambobin kungiyar kasashen da suke fitar da man fetur (OPEC) wajen kai ga cimma wata yarjejeniya, ta yadda za a iya daidaita farashin man fetur a albarkacin taron kungiyar da aka tsai da shiryawa a ranar 30 ga wannan watan a birnin Vienna na kasar Austria.
Domin daidaita kasuwanni, akwai bukatar ta aiwatar da yarjejeniya mai ma'anar tarihi ta Alger. Ina mai cike da imani da kyakkyawan fata na ganin gaskiya ta yi aikinta. Muna fatan za a cimma wata yarjejeniya ta gaskiya da adalci da za ta yi aiki wajen daidaita dukkan muhimman abubuwan da suka faru a cikin wasu kasashe mambobin kungiyar OPEC, har da kasashen da ba mamba ba, in ji mista A-Falih a yayin wata ganawa tare da takwaransa na kasar Aljeriya Noureddine Boutarfa, a cewar wata sanarwar da ma'aikatar makamashin Aljeriya ta bayar. (Maman Ada)