in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojan Iraki ta fara yunkurin sake kwato yammacin birnin Mosul
2017-02-20 09:51:44 cri

Jiya Lahadi ne firaministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya sanar da cewa, rundunar sojan kasarsa ta fara daukar matakai na sake kwato yammacin birnin Mosul.

Birnin na Mosul, wanda ke cikin manyan biranen kasar biyu, ya fada hannun 'yan tawayen IS tun cikin watan Yunin shekarar 2014. Sai dai a baya bayan nan rundunar sojan kasar ta soma daukar matakai na sake kwato shi.

Rundunar sojan kasar ta fara daukar matakan ne tun daga ranar 17 ga watan Oktobar bara, kafin daga bisani ta sanar da samun nasarar kwato gabashin birnin.

A halin yanzu mutane fiye da dubu 700 ne ke zaune a yammacin Mosul, wadanda yawancinsu ke fama da rashin abinci, kuma a ko da yaushe matsalar jin kai na iya barke a birnin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China