Haka kuma, ministan kiwon lafiyar kasar Adila Hammoud ya ce, gwamnatin kasar ta riga ta mika gawawwaki 115 ga iyalansu, a halin yanzu kuma, ana ci gaba da gudanar da binciken DNA kan sauran gawawwaki 177, domin tabbatar da asalinsu.
Kaza lika ya ce, fashewar boma-bomai a yankin ta kuma haddasa jikkatar mutane 200, kuma galibi daga cikinsu sun riga sun fita daga asibitoci, yayin da guda 23 suke ci gaba da karbar jinya.
Da safiyar ranar 3 ga wata, kungiyar IS ta kai hare haren boma-boman aka dasa cikin mota a yankin Karrada, lamarin da ya lalata wani babban kanti da wasu shaguna dake kusa da wurin, haka kuma, yankin Karrada shi ne daya daga cikin cibiyoyin kasuwanci dake cikin birnin Baghdad, shi ya sa, a lokacin fashewar boma-bomai, akwai mutane da dama dake sayayyar hidimar karamar sallah. (Maryam)