Yau Litinin ne, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi maraba da warware rikicin kasar Gambiya cikin lumana, ta kuma yi fatan cewa, sassa daban daban na kasar za su ba da muhimmanci ga muradun kasa da ta jama'arsu, za su kuma hada kai wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar da himmantuwa wajen farfado da kasar.
Rahotanni na cewa, MDD, AU, da ECOWAS sun ba da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka bayyan aniyarsu ta yin aiki da sabon shugaban Gambiya mista Adama Barrow. Tuni dai, dakarun sojan hadin gwiwar kasashen yammacin Afirka suka shiga kasar ta Gambiya, a kokarin tabbatar da ganin mista Adama Barrow ya koma kasar ya kama aiki lami lafiya. (Tasallah Yuan)