in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Gambiya za ta yi bikin cika shekaru 51 da samun 'yancin kai
2016-02-18 11:08:05 cri
Kasar Gambiya ta shirya tsab domin gudanar da bikin cikarta shekaru 51 da samun 'yancin kai a yau Alhamis.

Bikin, wanda ake sa ran gudanarwa a tsakiyar Serekunda birnin kasuwanci na kasar dake da tazarar kilomita 7 daga babban birnin kasar Banjul.

Dalibai 'yan makaranta za su gudanar da faretin nuna al'adun gargajiya na kasar.

Kasar Gambiya ta samu nasarar ballewa daga turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya a ranar 18 ga watan Fabrairun shekarar 1965, sannan ta kasance jamhuriya a shekarar 1973.

Za'a gudanar da wasannin motsa jiki da yammaci wannan rana, bayan kammala faretin.

Shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh, zai jagoranci bikin murnar samun 'yancin kan kasar, duk da irin bambamcin siyasa dake tsakaninsa da tsohuwar uwar gijiyarsa wato Birtaniya.

Shi dai shugaba Jammeh, ya janye kasarsa daga cikin ayarin kasashen renon Ingila, kuma ya kasance shugaban kasa na farko a Afrika, da ya fice daga kungiyar kasashen masu Magana da Ingilishi tun bayan ficewar shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe daga cikin kungiyar a 2003.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China