in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh ya bar kasar Gambia
2017-01-22 11:18:30 cri

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Gambia suka bayar, an ce, tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya tashi daga kasar zuwa birnin Conakry dake kasar Guinea a daren ranar 21 ga wata.

An ce, a filin jiragen sama na birnin Banjul na kasar Gambia, Jammeh ya shiga jirgin saman musamman tare da shugaban kasar Guinea Alpha Condé, kana jirgin saman na daban na kasar Mauritania mai dauke da iyalan Jammeh da masu bin shi, shi ma ya tashi a daidai wannan lokacin.

Shugaban kasar Gambia mai jiran gado Adama Barrow ya bayyana a daren ranar 21 ga wata cewa, Yahya Jammeh ya riga ya bar kasar Gambia. Kana ya ce, zai dawo kasar Gambia bayan da ya samu tabbaci a fannin tsaro.

A ranar 20 ga wata da tsakar rana, shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz da takwaransa na kasar Guinea, Alpha Conde, da tawagar wakilan kungiyar ECOWAS sun shiga-tsakani a birnin Banjul na kasar Gambia. A ranar 21 ga wata, Jammeh ya yi jawabi ta gidan telebijin na kasar Gambia cewa, ya sauka daga karagar mulkin kasar Gambia, kuma zai bar kasar ta Gambia. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China