in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AU ta yi maraba da rantsar da sabon shugban kasar Gambia
2017-01-21 12:10:38 cri
Tarayyar Afrika AU, ta yi maraba da bikin rantsar da sabon shugaban kasar Gambia Adama Barrow da aka yi a ranar Alhamis, tana mai taya shi murnar zama shugaban kasa.

Kungiyar, ta kuma yi kira ga dukkan mambobinta da sauran kasashen waje, su dauki Adama Barrow, a matsayin halastaccen shugaban kasar Gambia.

Kwamitin sulhu da wanzar da zaman lafiya na kungiyar, ya gudanar da wani taro a jiya Jumma'a, inda ya tattauna kan yanayin da ake ciki a kasar ta Gambia tun bayan gudanar da zabe.

Kwamitin ya bayyana kudurin kungiyar AU, na aiki tare da sabon gwamnatin kasar Gambia, wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da tabbatar da tsaro a kasar.

Sanarwar bayan taro da kwamitin ya fitar ta ce, kwamitin na sa ran Shugaba Adama Barrow zai halarci taron kungiyar AU karo na 28 da za a yi a ranakun 30 da 31 ga watan nan na Janairu a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha wato Ethiopia.

Sanarwar ta kuma jaddada goyon bayanta ga matakin da ECOWAS ta dauka yayin taronta da ya gudana a Abuja babban birnin Nijeriya, wanda ya hada da daukar dukkan matakan da suka wajaba wajen ganin an mutunta muradun al'ummar Gambia. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China