in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An baiwa Yayah Jammeh damar karshe kafin amfani da karfin tuwo
2017-01-20 20:49:06 cri

Tawagar dakarun hadin gwiwa na kungiyar ECOWAS, ta dakatar da kutsawa kasar Gambia, a wani mataki na karshe da aka baiwa shugaba Yayah Jammeh, na ya sauka daga karagar mulki, ya kuma mika ragamar kasar ga sabon shugaban ta Adama Barrow.

Da yake karin haske game da wannan mataki, kwamishina a ofishin kungiyar ta ECOWAS Marcel Alain Da Souza, ya ce an baiwa dakarun kungiyar umarnin dakatawa, domin baiwa Jemmeh wannan dama a daren jiya Alhamis, da nufin cimma nasarar mika mulkin kasar ga sabon shugaban ta cikin ruwan sanyi.

Da Souza ya ce dakarun kasar Senegal, dake samun goyon bayan takwarorin su na wasu kasashen yammacin Afirka, sun isa kasar Gambia da yammacin ranar Alhamis, da nufin tursasa shugaban Jammeh ya mika mulki ga Barrow, wanda tuni ya sha rantsuwar kama aiki a ranar Alhamis a birnin Dakar na kasar Senegal.

An dai tanaji dakarun soji 7000 domin wannan aiki, na tabbatar da wanzuwar dimokaradiyya a Gambia.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China