in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da Adama Barrow a matsayin shugaban kasar Gambia a Senegal
2017-01-20 10:50:34 cri

An rantsar da Adama Barrow a matsayin shugaban kasar Gambia jiya, a ofishin jakadancin Gambia dake Dakar, babban birnin kasar Senegal.

An rantsar da Adama Barrow ne a gaban Sheriff Tambedou, shugaban kungiyar lauyoyi ta Gambia, inda hakan, ya bashi damar kasancewa shugaban kasar Gambia na uku, tun bayan Dauda Jawara da ya yi mulki daga 1970 zuwa 1994, da kuma shugaban kasar mai ci Yahaya Jammeh wanda ya hau karargar mulki bayan juyin mulki da aka yi a shekarar 1994.

Bikin rantsuwar, ya samu halatar Firayiministan Senegal Muhammad Dionne da jakadun kasashen waje dake Senegal da kuma jami'an kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma wato ECOWAS.

A jawabinsa, Shugaba Barrow ya yi kira da a samar da hadin kan kasa, ya na mai yabawa al'ummar Gambia, inda ya ce wannan ne karon farko da kasar ta sauya gwamnati ta hanyar zabe.

Ya kuma yi kira ga Yahaya Jammeh, ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar, yana mai tabbatar da cewa, nan bada jimawa ba, zai kafa gwamnatinsa tare da komawa Gambia.

Yahaya Jameh ya ce zaman lafiya suke muradi, kuma suna kira ga kowa ya rungumi zaman lafiya. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China