in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jammeh ya mika ragamar mulkin kasar Gambia
2017-01-21 17:42:03 cri
Yahya Jammeh ya yi jawabi ta gidan telebijin na kasar Gambia a yau Asabar 21 ga wata, inda ya sanar da mika mulkin shugabancin kasar.

Bayan shafe sa'o'i da shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz da takwaransa na kasar Guinea, Alpha Conde, da suka shiga-tsakani don warware rikicin kasar Gambia cikin lumana, Jammeh ya bayyana godiya ga jama'ar kasar, inda ya kuma tsaida kudurin mika mulki.

Jammeh ya bayyana cewa, ana iya warware dukkan matsalolin da ake fuskanta cikin lumana, kana ya yi imani da cewa, jama'ar kasashen Afirka za su iya cimma matsaya da kansu, don tabbatar da kafuwar demokuradiyya da bunkasar tattalin arziki da zamantakewa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China