in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Adama Barrow ya ce Yahya Jammeh ya amince ya sauka daga karagar mulki
2017-01-21 12:23:10 cri

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow, ya wallafa a shafinsa na Twitter a jiya da dare cewa, tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh, ya amince ya sauka daga karagar mulki tare da ficewa daga kasar.

A jiya da rana ne shugabannin kasashen Mauritania da Guinea suka isa babban birnin kasar Gambia wato Banjul, a wani yunkuri na karshe, na bada baki ga Jammeh, domin ya mika mulki ga Adama Barrow, tun kafin dakarun kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS karkashin jagorancin dakarun Najeriya da Senegal, su shiga tsakani.

Zuwa yanzu, babu wani bayani game da inda Jammeh zai tafi, sai dai, kasashen Morocco da Najeriya da Mauritania da kuma Guinea, sun bayyana aniyarsu ta karbar sa.( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China