in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin Olympic ya kulla huldar hadin gwiwa da kamfanin ALIBABA
2017-01-20 11:25:50 cri

Jiya Alhamis, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa watau IOC da kamfanin ALIBABA suka sanar da kulla huldar hadin gwiwar abokantaka a tsakaninsu ta dogon lokaci a birnin Davos na kasar Switzerland, lamarin da ya nuna cewa, kwamitin IOC zai yi hadin gwiwa da kamfanin ALIBABA a fannin intanet mai suna"Cloud Service" da kuma hada-hada ta hanyar zamani, a sa'i daya kuma, kamfanin ALIBABA zai hada kai da kwamitin na OIC don bullo da wata kafar sadarwar wasannin Olympics.

Haka kuma, babban jami'in kamfanin ALIBABA Zhang Yong ya bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2028, kamfaninsa zai taimaka wa kwamitin kare 'yancin mallaka, sa'an nan, zai bullo da wani dandalin hada-hada ta hanyar zamani na wasannin Olympics na kasa da kasa. A sa'i daya kuma, kwamitin zai tsara da kuma kyautata hanyar sadarwar wasannin Olympic ga al'ummar kasar Sin tare da yin amfani da fasahohin zamani na kamfanin ALIBABA a fannin inganta kafofin watsa labarai na intanet.

A yayin taron maneman labaran da aka yi a wannan rana, shugaban kwamitin IOC Thomas Bach ya yi imani cewa, kamfanin ALIBABA zai taimaka wa kwamitin nasa wajen kyautata ayyukansa yadda ya kamata a nan gaba.

Bugu da kari, shugaban hukumar direktocin kamfanin ALIBABA Ma Yun ya ce, kamfaninsa zai ci gaba da kyautata ayyuka da fasahohinsa da abin ya shafa domin goyon bayan kwamitin Olympic ta yadda zai shirya gasar Olympics ta 2020 cikin nasara, tare kuma da ci gaba da raya wasannin Olympics yadda ya kamata ta yadda zai dace da zamani. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China