in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar wasan kwallon raga ta mata ta Sin ta samu lambar yabo ta zinari a gasar Olympics
2016-08-21 13:15:56 cri

Yau Lahadi, an kammala gasar wasan kwallon raga ta mata a gasar wasannin Olympics da ake gudanarwa a birnin Rio na kasar Brazil, inda kungiyar wasan kwallon raga ta mata ta kasar Sin ta samu lambar yabo ta zinari cikin wannan gasa, watau bayan shekaru 12, kungiyar wasan kwallon raga ta mata ta kasar Sin ta sake rike wannan matsayi na zakara cikin gasar wasannin Olympics.

Kungiyar wasan kwallon raga ta mata ta kasar Sin ta taba samun lambar yabo ta zinari a gasar wasannin Olympics da aka yi a birnin Los Angeles na kasar Amurka a shekarar 1984, da kuma gasar da aka yi a birnin Athens na kasar Greece a shekarar 2004. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China