Haka kuma, ya nuna yabo matuka kan yadda sabbin kafofin watsa labarai suke watsa labaran wasannin na Olympics, lamarin da ya sa gasar da ake yi na wannan karo a birnin Rio ta kasance mafi yaduwa da mafi samun karbuwa, kana, ya ce, abu mai muhimmanci shi ne, ba kawai mutane suna kula da menene aka yi cikin gasar ba, har ma ana mai da hankali kan yin musayar ra'ayoyi a tsakanin juna.
Da farko IOC ya taba nuna shakku kan kasar Brazil na yiwuwar shirya wannan gasar, amma Bach ya ce, bai taba sake yin tunani kan ko zai baiwa kasar Brazil damar karbi bakuncin shirya wanann gasar ba ko a'a, sabo da a kullum yana ganin cewa, gasar Olympics da ake yi a birnin Rio na kasar Brazil ta zama abu mai kyau wajen bunkasa harkokin wasanni na duniya. (Maryam)