Ministan kula da harkokin labarai na kasar Zimbabwe ya ce, wannan shi ne labarin karya, kuma labari ne da babu tushen gaskiya cikin sa.
Ya bayyana haka ne a yayin dake halartar wani bikin ba da kyautar kudin karatu da wani kamfanin kasar Sin ya samar wa daliban Zimbabwe.
Kaza lika, ya ce, ba ko wane dan wasa ya iya cimma lambar yabo cikin gasar wasannin Olympics ba, amma muna alfahari da dukkan 'yan wasan kasar da suka shiga gasar Olympics, duk da ko wane irin sakamako suka samu a gasar da aka yi.
Wasu kafofin watsa labaran Nijeriya sun ce, shugaban kasar Zimbabwe ya ba da umurni kama 'yan wasan kasar da suka shiga gasar wasannin Olympics a filin jirgin saman kasar, sabo da ba su samu lambobin yabo a yayin gasar Olympic da aka yi a birnin Rio na kasar Brazil. (Maryam)