in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar 'yan wasa ta Sin ta lashe lambar zinare ta gasar tseren keke a filin wasa ta kungiya-kungiya ta mata
2016-08-13 14:17:31 cri

A jiya Jumma'a, an shiga rana ta 7 ta gasar Olympics ta Rio, tawagar 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta Sin ta samu sakamako masu kyau. A yayin gasar tafiya cikin sauri ta tsawon kilomita 20 ta maza da aka yi a wannan rana da yamma, dan wasan Sin Wang Zhen ya lashe lambar zinare da awa 1 da minti 19 da dakika 14. Kuma abokin wasansa wanda ma daga tawagar kasar Sin Cai Zelin ya lashe lambar azurfa.

Bugu da kari, 'yan wasan tseren keke a filin wasa na kasar Sin sun samu sakamako mafi kyau a cikin tarihi, inda Gong Jinjie da Zhong Tianshi sun lashe lambar zinare ta gasar tseren keke a filin wasa ta kungiya-kungiya ta mata.

Ban da haka kuma, a ran nan da aka fara gasannin guje-guje da tsalle-tsalle, 'yar wasa ta kasar Habasha Almaz Ayana ta lashe lambar zinare a cikin gasar guje-guje ta mata ta tsawon mita dubu 10 da minti 29 da dakika 17 da kasa da dakika 45, wannan sakamako ya karya tsohon matsayin bajinta na duniya da 'yar wasan kasar Sin Wang Junxia ta kafa da minti 29 da dakika 31 da kasa da dakika 78 a shekarar 1993.

Ya zuwa jiya Jumma'a da dare, tawagar 'yan wasa ta Sin tana matsayi na biyu da lambobin zinare 13 da na azurfa 9 da kuma na tagulla 14. Kasar Amurka tana kan gaba da lambobin zinare 16, kana kasar Japan tana matsayi na 3 da lambobin zinare 7.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China