in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta 31 a Brazil
2016-08-22 11:37:36 cri

A jiya Lahadi 21 ga watan nan ne aka rufe gasar Olympics ta 31 a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, inda kasahen Amurka, da Birtaniya, da Sin suke sahun gaba ta fuskar lambobin yabo na zinariya.

An gudanar da bikin rufe gasar ne a filin wasan motsa jiki na Maracana, wanda shi ne masaukin gasar da kasar Brazil ta karbi bakunci, inda aka gabatar da raye-raye, da wake-wake masu salon Samba, domin murnar cimma nasarar gudanar gasar cikin nasara.

A cikin jawabin da ya gabatar, shugaban kwamitin Olympics na kasa da kasa Mista Thomas Bach, ya bayyana cewa, an gudanar da gasar mai ban mamaki a wani birni mai ban mamaki.

Wannan ne karo na farko da aka gudanar da gasar a nahiyar kudancin Amurka, wannan gasa ta tsawon kwanaki 16 ta samu halartar 'yan wasannin motsa jiki fiye da dubu 10 daga kasashe 206. Ban da wannan kuma, kwamitin ya kafa wata tawaga mai kunshe da 'yan gudun hijira 10, don yin kira game da kiyaye zaman lafiya a duniya.

Za dai a gudanar da gasar ta Olympics mai zuwa ne a birnin Tokyo na kasar Japan bayan wasu shekaru 4. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China