Bisa shirin sayar da hannayen jari miliyan 320 a kasar Amurka, yawan kudin da kamfanin Alibaba zai tanada ta wannan hanya zai kai biliyan 21.8, wanda zai kasance kamfanin mafi samun kudi ta hanyar sayar da hannayen jarinsa a karon farko wato IPO a kasar Amurka. Idan kamfanin ya yi amfani da ikon kara sayar da hannayen jari, yawan kudin da kamfanin zai samu zai kai dala kimanin biliyan 25, ta haka kamfanin zai zama kamfanin mafi samun kudin hannayen jari na IPO a fadin duniya.
Bisa shirin da aka yi, za a fara sayar da hannayen jari na kamfanin Alibaba a kasuwar musayar takardun hada-hadar kudi dake birnin New York a ranar 19 ga wata, kana takensa a wannan kasuwa ita ce "BABA". (Zainab)