Na daya, kasar Sin za ta ci gaba da manufarta, ta gudanar da ziyara a kasashen Afirka a cikin farkon ko wace shekara, sabo da kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka, su ne babban tushen aikin diflomasiyyar kasar Sin.
Na biyu, kasar Sin na fatan kasashen Afirka za su hada kai domin fuskantar da sabbin kalubalolin duniya, kamar yadda ita ma kasar Sin ke fatan karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka, ta yadda za ta ba da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya, da bunkasuwar kasashen Afirka.
Na uku, kasar Sin tana fatan hada kan kasashen Afirka wajen neman sabbin hanyoyin kyautata hadin gwiwa tsakaninsu, ta yadda za a bude wani sabon shafin hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu, wanda zai dace da bunkasuwar duniya. (Maryam)