Wang Yi: ana samun sabbin canji a fannoni uku kan hadin gwiwar samun moriyar juna dake tsakanin Sin da Afirka
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, bisa sabon tunanin da aka gabatar a gun taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2015, ana samun sabbin canji a fannoni uku kan hadin gwiwar samun moriyar juna a tsakanin Sin da Afirka. Mr. Wang wanda ya zayyana wadannan fannoni yayin da yake ganawa da 'yan jarida tare da ministan harkokin wajen kasar Zambia Harry Kalaba a jiya Lahadi, ya ce na farko, an canja daga matakin hadin gwiwa bisa jagorancin gwamnati, zuwa yanayin kasuwa. Sai na biyu, sauyin da aka samu daga cinikin kaya zuwa hadin gwiwar samar da kayayyaki da inganta cinikin samar da kayayyakin kerawa. Kana na uku, an canja daga daukar alhakin gudanar da aiki zuwa zuba jari da gine gine. Ya ce yanzu haka ana inganta tunani, da tsari kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka bisa yanayin da ake ciki.
Haka zalika kuma, Wang Yi ya yi nuni da cewa, koda yake aka samun canji a yananin duniya da tattalin arzikin duniya, Sin za ta cika alkawarinta na aiwatar da kudurorin da aka cimma, a gun taron koli na Johannesburg tare da kasashen Afirka, don amfanar jama'ar Sin da Afirka cikin hanzari. (Zainab)