in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin waje na Sin ya yi shawarwari da takwararsa ta Madagascar
2017-01-08 13:27:49 cri

A jiya Asabar 7 ga wata, ministan harkokin waje na Sin Wang Yi ya yi shawarwari da takwararsa ta Madagascar, madam Béatrice Atallah a birnin Antananarivo.

A yayin ganawarsu, Wang ya bayyana cewa, akwai wata al'ada a fannin diplomasiyyar kasar Sin, wato a kowace shekara ministan harkokin waje na kasar ya kan kai ziyararsa a karo na farko zuwa nahiyar Afirka. Wannan ne alamar diplomasiyyar kasar, wadda ta nuna cewa, Sin tana daukar kasashe masu tasowa a matsayin babban tushe a fannin diplomasiyya, yayin da take sada zumunci da kasashen Afirka a karon farko.

Ban da haka, Wang ya bayyana cewa, a gun taron kolin Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shirin hadin gwiwa guda 10 bisa babban makasudi na sa kaimi ga raya masana'antu da aikin gona na zamani a nahiyar Afirka. Sin ta shawarci bangarorin biyu da su yi amfani da zarafin tabbatar da sakamakon taron kolin Johannesburg da sa kaimi ga hadin gwiwa kan shirin "Ziri daya da hanya daya", su yi hadin gwiwa tsakaninsu, musamman ma a fannonin aikin gona, da sha'anin kere-kere, da yawon shakatawa, da kuma zirga zirgar jirgin sama a shiyya shiyya bisa bukatun Madagascar, domin samun moriyar juna, tare da kafa manyan kayayyakin amfanin jama'a, da horar da kwararru, da kuma zuba jari kan cinikayya yadda ya kamata.

A nata bangare, minista Béatrice Atallah ta bayyana cewa, Madagascar tana alfahari sosai da ganin cewa, minista Wang Yi ya kai ziyararsa a karo na farko zuwa kasar a shekarar 2017. Kuma Madagascar ta amince da shawarar da Sin ta bayar. Tana matukar wadannan fannoni. Shi ya sa take maraba da kamfanonin Sin da su zuba jari a kasar. Da fatan za a sa kaimi ga bunkasuwa cikin kasa bisa hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China