in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da takwaransa na Nijeriya
2017-01-12 10:19:15 cri

Jiya Laraba ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na Nijeriya Geoffrey Onyeama a Abuja, babban birnin kasar.

A yayin ganawar tasu, Wang Yi ya ce, kasar Sin ita ce kasa mai tasowa mafi girma a nan duniya, yayin da Nijeriya ta kasance kasa mai tasowa mafi girma a nahiyar Afirka. A 'yan shekarun nan, kasashen biyu na ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakaninsu, lamarin da ya sa shi kasancewa kan gaba cikin hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Wang Yi ya gabatar da shawarwari biyar wajen ci gaba da zurfafa dangantakar sassan biyu da za su hada da kiyaye manufar kasar Sin daya tak domin karfafa fahimtar siyasa tsakanin kasashen biyu, da kyautata tsarin cin moriyar juna, da na ayyukan kiyaye tsaro a Nijeriya, da musayar al'adu, da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa domin kiyaye moriyar kasashe masu tasowa.

A nasa bangaren, Mr. Onyeama ya ce, ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan kai ziyarar aiki kasashen Afirka cikin farkon shekara, lamarin da ya bayyana a matsayin aniyar kasar Sin ta karfafa zumuncin dake tsakaninta da kasashen Afirka.

A halin yanzu, Nijeriya ta dukufa wajen bunkasa ayyukan masana'antun dake kasar domin rage dogaro kan man fetur, tare da raya tattalin arzikinta bisa fannoni daban daban, inda take sa ran samun taimako daga kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China