in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya gana da wakilin musamman na shugaban Sin
2017-01-10 10:22:07 cri
Shugaban kasar Ghana Akufo Addo, ya gana da wakilin musamman na shugaban kasar Sin Wang Zhengwei a fadar shugaban kasar dake birnin Accra.

A yayin ganawar tasu, Wang Zhengwei ya mika kyakkyawan fatan shugaba Xi Jinping ga Mr. Akufo Addo. Sa'an nan, ya ce, an sami sakamako masu gamsarwa da dama, bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Ghana, tun bayan kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu a shekarar 1960.

Ya ce, cikin 'yan shekarun nan, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin gina ababen more rayuwa, da samar da wutar lantarki, da jirga-jirgar jiragen sama da dai sauransu, sun ba da tallafi ga al'ummomin kasashen biyu kwarai da gaske. Haka kuma, kasar Sin ta mai da hankali sosai wajen raya dangantakar dake tsakaninta da Ghana, inda take sa ran karfafa fahimtar siyasa a tsakaninsu, yayin da kuma take kara habaka hadin gwiwa da musayar al'adu a tsakaninsu, ta yadda za a daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare kuma, shugaba Akufo Addo bayyana godiyar sa ya y i ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, da kuma wakilin musamman da shugaba Xi ya tura zuwa kasar Ghana, domin halartar bikin rantsar da shi.

Ya ce, kasar Sin abokiyar arziki ce ta Ghana, an sami sakamako mai kyau bisa hadin gwiwar kasashen biyu cikin dogon lokacin da ya gabata. Don haka Ghana ke godiya matuka dangane da taimakon da kasar Sin ta samar gare ta a fannin raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma, tana mai fatan ci gaba da zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin bisa fannoni daban daban, ta yadda za a ci gaba da karfafa dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China