in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan kasar Sin a Ghana ya ba da lambar yabo ga dalibai masu kaifin basira
2015-11-19 10:48:48 cri

Jakadan kasar Sin a kasar Ghana a Sun Baohong, a ranar Larabar nan ya ba da lambar yabo ga wasu dalibai 28, wadanda suka kware wajen koyon harshen Sinanci da al'adun Sinawa a jami'ar Ghana dake Accra.

Jakadan na kasar Sin ya ba da lambobin yabo ga daliban ne masu kaifin basira domin kara azama kan samun karin daliban kasar Ghana da za su koyi harshen Sinanci da sanin al'adun Sinawa, don hakan zai ba da daliban damar shiga al'amurran da ba na gwmnati ba wadanda suka shafi muyasar al'adu da huldar cinikayya tsakanin kasashen Ghana da Sin bayan kammala karatunsu.

Tun bayan bullo da shirin ba da kyautukan lambobin yabon shekaru 4 da suka gabata, kawo yanzu an bai wa daliban jami'ar Ghana sama da 60 kyautukan lambobin yabon, lamarin da ya yi sanadiyyar samun karuwar dalibai masu sha'awar koyon harshen Sinanci.

Mista Sun ya bukaci daliban da su jajurce wajen nakaltar harshen Sinanci, domin a cewarsa, zai ba su damar bayar da gudummowarsu wajen ci gaban tattalin arzikin kasashen biyu.

Ko wane dalibi ya samu takardar sheda da kyautar kudi wanda ya kama daga dalar Amurka 300 zuwa 600. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China