in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaban Sin zai halarci bikin rantsar da shugaban Ghana
2017-01-04 18:51:53 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya sanar a yau Laraba 4 ga wata a nan Beijing cewa, bisa gayyatar gwamnatin kasar Ghana, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Wang Zhengwei, wanda ke matsayin manzon musamman na Xi Jinping, shugaban kasar Sin, zai halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, wanda za a gudanar a ranar 7 ga wata a birnin Accra, fadar mulkin kasar ta Ghana. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China