in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabanni daga kasashen Afirka da Turai ne za su halarci bikin rantsar da shugaban kasar Ghana
2017-01-04 10:57:13 cri
Rahotanni daga kasar Ghana na nuna cewa, kimanin shugabanni 12 daga kasashen Afirka da Turai ne ake saran za su halarci bikin rantsar da shugaban kasar Ghana da aka zaba, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, da za a yi a a ranar 7 ga watan Janairu.

Tawagar shirin mika mulkin shugaban kasar ta Ghana wadda ta bayyana hakan a jiya Talata, ta kuma sanar da cewa, shugaba Alassane Ouattara na kasar Cote d'Ivoire ne zai kasance bako mai jawabi a yayin bikin, wanda ake saran zai samu halartar wasu wakilan gwamnatoci 13 da wakilan kungiyoyin kasa da kasa 5 da wasu tsoffin shugabannin kasashen yammacin Afirka da na wasu sassa na duniya.

Wakiliya a tawagar shirin mika mulkin Shirley Ayorkor Botwe ta bayyana cewa,za a gudanar da bikin rantsar da shugaba Addo ne a dandalin Black Star da ke Accra,babban birnin kasar. Ana kuma saran za a girke jami'an tsaro kimamin 5,000 a yayin bikin, a wani mataki na magance duk wata matsala da ka iya tasowa.

Nana Akufo-Addo dai ya kayar da shugaba John Dramana Mahama ne a babban zaben kasar na watan da ya gabata, bayan da ya samu kaso 53.8 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada, yayin da shi kuma Mahama ya samu kaso 44.4 cikin 100.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China