in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zababben Shugaban kasar Ghana ya sanar da nadin wasu jami'an Gwamnatinsa
2017-01-05 10:46:17 cri
A jiya Laraba ne zababben shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya sanar da nadin wasu jami'an Gwamnatinsa, da za su taimaka masa wajen cimma muradun al'ummar kasar a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Yayin wani taron manema labarai da ya yi a fadarsa, Akufo-Addo ya sanar da nadin Akosua Frema Opare-Osai a matsayin shugabar ma'aikatan ofishin Shugaban Kasa.

Opare Osei ta kasance mace ta farko da za ta rike wannan mukami a kasar tun shekarar 1992

Haka zalika, zababben shugaban, ya nada Albert Kan Dapaah, tsohon Ministan harkokin cikin gida karkashin shugabancin John Agyekum Kufuor, a matsayin ministan tsaron kasar.

Yayin wani biki da za a yi a ranar Asabar a birnin Accra ne za a rantsar da shugaba Akufo-Addo. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China