in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da sabon shugaba kasar Ghana Akufo-Addo
2017-01-08 13:27:22 cri

A jiya Asabar sabon zababben shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya sha rantsuwar kama aiki, inda ya sha alwashin farfado da tattalin arzikin kasar da kuma adana dukiyar gwamnati.

Babbar jojin kasar Georgina Theodora Wood, ita ce ta rantsar da sabon shugaban, wanda ya samu halartar shugabannin kasashen Afrika 12, da manyan jami'ai daga kasashen duniya da dama.

Akufo-Addo ya ce, gwamnatinsa zata rage kudaden haraji a matsayin wata hanyar farfado da cigaban tattalin arzikin kasar da bada fifiko ga kamfanoni masu zaman kansu domin samun cigaba da samar da guraben ayyukan yi ga jama'a.

Yace kasar Ghana ba zata sauka daga turbar matsayinta na kasa mai tasowa ba, kana ya bukaci jama'ar kasar su ba shi goyon baya domin tabbatar da ganin an samu canjin da jama'a suke zaba a watan da ya gabata.

Shi dai Akufo-Addo, mai shekaru 72 a duniya, tsohon lauya ne mai fafutukar kare hakkin bil adama, ya yi alkwarin samar da ilmi kyau a manyan makarantun kasar, baya ga alkawarin da yayi na samar da karin masana'antu a kasar. Ya karbi mulki ne daga hannun John Dramani Mahama, wanda yayi wa'adi mulki daya.

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara, wanda ya halarci bikin rantsuwar, ya bukaci al'ummar kasar Ghana da su cigaba da kare tsarin mulkin demokaradiyyar kasar, yana mai cewa, yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar cikin lumana, da kuma mika mulkin lami lafiya ga sabuwar gwamnati, ya kara daga kimar kasar a idanun duniya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China