in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi tir da harin ta'addanci da aka yi a Istanbul da Alkahira
2016-12-12 20:23:51 cri

A yau Litginin ne Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi tir da babbar murya kan hare-haren ta'addanci da aka kaddamar a biranen Istanbul da Alkahira a kwanan baya, ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata sakamakon hare-haren.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana Allah-wadai da duk wani nau'in ta'addanci, kana tana son ci gaba da goyon bayan kokarin da kasashe masu ruwa da tsaki suke bayarwa wajen tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro da kuma yaki da ta'addanci. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China