in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa na fama da barazanar hare-haren ta'addanci mafi tsanani, in ji firaministan kasar
2016-09-12 10:16:15 cri

Firaministan kasar Faransa Manuel Valls ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasar na fama da barazanar hare-haren ta'addanci mafi tsanani, yawan Faransawan dake da ra'ayin ta'addanci da 'yan sanda suka kididdige ya kai kimanin dubu 15.

Manuel Valls ya ce, a halin yanzu akwai mutane 1350 da ake tsare da su a kasar Faransa bayan da aka yi bincike a kan su, 293 daga cikinsu suna da alaka da kungiyoyin ta'addanci kai tsaye. Ban da haka kuma, akwai masu tsattsauran ra'ayi 700 'yan kasar Faransa da suka tafi kasashen Iraki da Syria domin shiga ayyukan ta'addanci, ciki har da mata 275 da kuma yara da dama. Manuel Valls ya ce, ra'ayin ta'addanci shi batun da Faransanwa ke kokarin magancewa.

Bugu da kari, Manuel Valls ya kara da cewa, hukumar leken asiri da 'yan sanda ta kasar Faransa suna daukar matakan dakile ra'ayin ta'addanci yadda ya kamata, kuma a ko wace rana suna farautar 'yan ta'adda. A kwanakin baya ma sun dakile wasu hare-haren ta'addanci biyu da aka shirya kaiwa. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China